2 Oktoba 2014 - 10:04

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar ta sanar da cewa tana shirin fara tattaunawa da kungiyoyi masu dauke da makami na kasar Libiya da nufin bukatarsu da su ajiye makamansu da kawo karshen rikicin da ke faruwa a kasar.

Manzon MDDn na musamman sannan kuma shugaban tawagar ayyukan MDDn a kasar Libiya Bernardino Leon ne ya sanar da hakan inda ya ce majalisar tana shirin fara tattaunawa da masu dauke da makamin da nufin kawo karshen yakin da ke gudana a kasar tsakanin bangarori daban-daban masu dauke da makami da kuma dakarun gwamnati.

 

Manzon MDDn ya kara da cewa manufar wannan tattaunawar dai a matakin farko ita ce ganin masu dauke da makamin sun fice daga cikin garuruwa da kuma amincewa da jami’an tsaron gwamnati, sai dai ya ce akwai tsananin wahala cikin cimma hakan.

 

Tun dai bayan kifar da gwamnatin tsohon shugaba Kanar Mu’ammar Gaddafi kasar Libiyan ta shiga tsaka mai wuya na mulki da tsaro ta yadda aka gagara kafa wata gwamnati tsayayyiya da za ta iya gudanar da kasar. ABNA